21/10/2023
Wike bazai rushe wani tsagi na babban Masallacin Abuja ba, amma zai kwace manyan Fulotan masallacin kuma yace zai biya diya.
Na bibiyi yadda case din batun rushe wani sashi na babban Masallacin Abuja da babban Ministan Abuja Wike yayi yinkurin yi.
A bincikena kan yadda lamarin yake shine; Tun a watan Satumba Nyesom Wike ya baiwa masu fulotai kimanin 200 a tsakiyar Abuja, wa'adin wata uku su fara ginawa, ko kuma su fuskanci yiwuwar soke ikon mallaka da aka ba su.
Matakin da mai yiwuwa zai shafi wuraren ibada da dama a birnin, ciki har da babban masallaci na kasa. Ana tsakiya da batun, sai maganar aikin fadada wani t**i mai makwabtaka da babban Masallacin Abuja ya taso, wanda rahotanni s**a tabbatar da sai an bukaci rushe wani sashi na Babban Masallacin Abuja, don cimma burin fadada t**in.
Kasantuwar mutanan mu na Arewa sun ankara an fara cece-kuce hankalinmu duk ya koma kan batun, musamman a kafofin sada zumunta na Najeriya, wanda ba'a san inda lamarin zai kai ba, hakan yasa Wike ya hakura ya janye kudirin shi na rushe wani sashi na Masallacin. Kamar yadda a jiya suma muhukuntan masallacin s**a fitar da sanar cewa Wike bazai rushe wani sashi na babban Masallacin ba.
A yanzu haka Wike ya tsaya kan batun kwace wasu daga cikin fulotan masallacin, domin yin aiki a wurin da suke, wanda kuma yayi alkawarin biyan diyya.
Daga Comr Abba Sani Pantami