Zinariya hausa

  • Home
  • Zinariya hausa

Zinariya hausa Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zinariya hausa, Newsstand, .

ALIYU NATA ANGO
21/08/2022

ALIYU NATA ANGO

LOKACINDA YAKE HANNUN TALAU CI KAFIN YA SAYARWA YAN NIGERIA
13/08/2022

LOKACINDA YAKE HANNUN TALAU CI KAFIN YA SAYARWA YAN NIGERIA

30/07/2022
KADAN DAGA CIKIN MATSALOLIN DA AKE SAMU WAJEN SHAYAR DA YARO NONO!! ⬇Tabbas iyaye diyawa sunayin kurakurai da dama wajen...
05/07/2022

KADAN DAGA CIKIN MATSALOLIN DA AKE SAMU WAJEN SHAYAR DA YARO NONO!!

Tabbas iyaye diyawa sunayin kurakurai da dama wajen shayar da yaro, ga kadan daga ciki :

1- Basa barin bakin Nonon yashiga bakin yaron gabaki daya.
Amfiso idan za ashayar da yaro nono , bakin nono wajen bakinnan duk yashiga bakin yaro, Sabida idan baishiga bakinsa sosai ba, yana shan iska, wannan iskan shi yake saka Yara kumburin ciki wani lokoci harda hararwa.

2- Shayar da yaro a kwance : Ba daidai bane a shayar da yaro a kwance , sabida akoi hanyar da ta hada Makwagoro, Kunne Da Hanci , To ta wannan hanyar ruwan nono yakan bi yaje kunne wanda hakan yana kawo ciwon kunne na yara.

3- Canzawa yaro nono : za kaga mata da dama idan sunsa yaro a daya Nonon tuni za kaga suncire sun maida zuwa daya Nonon.
Amfison idan ansa yaro a nono abarshi yai tashan daya Nonon har sai yakoshi, dalili kuwa bincike Ya nuna yaro idan yafara shan nono, Ruwan Nonon Farko da zaizo ruwa ne kadai, sai ruwan yagama zuwa abincin zaizo. Kinga kuwa idan Kinyi saurin maida shi zuwa daya Nonon kin chika cikinsa da ruwa babu abinci sai kiga yaro cikin dare yana kukan yinwa ke kina tunanin ciwon ciki ne kiyi ta dura masa magani a banza.

4- Bawa Yara kanana ruwa kafin wata shida : Tabbas duk wani ruwa da za'abawa yaro kafin wata shidda zai iya cutar da yaro, kuma gurbaccecen ruwa ne, idan ruwan randa ne akoi cututtuka wanda ido baya gani idan babba yasha zai iya jurewa amma yaro bashida garkuwan jikin da zai karesu, idan ruwan Faro ne ma akoi chemicals a ciki, yana daga cikin illar bada ruwa duk yaron da akabashi ruwa bazai barshi nono Ya isheshi ba.

Kadan daga cikin amfanin shayar da yaro nono Zallah har zuwa wata shida :

1- Yana Kara musu basira
2- Yana Kara musu garkuwan jiki
3- Yana karesu daga cututtuka
4- Yana Kara musu Ilmi.
5- Yana Hana yaro mummunar Kiba da mummunar ramewa.
6- Yana Kara soyayya tsakanin uwa da da.

INA KUKE MATASA MASU NEMN NA KAN SU. TAU GA DAMA TA SAMU. DIK MAI SHA AWAR GINA WEBSITE DON NEMAN KUDI TAU GA MAGINI WAN...
04/07/2022

INA KUKE MATASA MASU NEMN NA KAN SU. TAU GA DAMA TA SAMU. DIK MAI SHA AWAR GINA WEBSITE DON NEMAN KUDI TAU GA MAGINI WANDA ZAI TSARAMAKA WEBSITE TA YADDA ZAKA SAMU TALLAR AMINCEWAN ADSENSE CIKIN SAUKI. KAI SAURI KA SHIGA WANN LINK DIN TIN KAFIN YA CIKA

https://chat.whatsapp.com/LuKKAPekTmXC9paZp30Wrz

WhatsApp Group Invite

KUNA GANIN YA FADI GASKIYA KUWA?????
02/07/2022

KUNA GANIN YA FADI GASKIYA KUWA?????

DA DUMI-DUMI: An Bude Akwati Ta Biyu Da Aka Gano A Gidan Tsohon Hafsan Sojoji, Gidan Buratai, Akwatin Makare Take Da Kud...
28/06/2022

DA DUMI-DUMI: An Bude Akwati Ta Biyu Da Aka Gano A Gidan Tsohon Hafsan Sojoji, Gidan Buratai, Akwatin Makare Take Da Kudaden Kasashen Waje $170,0000, £85,000 da €54,000

Daga - Daily True Hausa News

Daga karshe jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC sun samu nasarar bude akwati na biyu da aka gano a gidan wani tsohon hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya).

A kwanakin baya ne jami’ai s**a fasa gidan a unguwar Wuse da ke Abuja inda aka kwato kudade da aka ware domin sayen mak**ai domin yaki da ta’addanci, motoci da sauran kayayyaki.

Sahara ta gano akwatin na biyu da aka bude kwanan nan yana dauke da $170,0000, £85,000 da €54,000.

Jaridar ta ruwaito a ranar Asabar ta musamman cewa an gano akwatuna biyu a gidan amma jami’an ICPC sun samu damar bude guda daya kawai. Jami’an sun kasa bude akwatin na biyu a lokacin da ake gabatar da rahoton.

Buratai, duk da musantawar da lauyansa da wasu s**a yi, tuni ya amince wa wata jarida cewa kadarorin nasa ne, kuma ba a bada takardar neman bincike ba kafin a kai samame.

“Ba wannan ne karon farko da Buratai ke cikin irin wannan badakala ba. Batun farko na Buratai shi ne wani dan kasuwa da ya tunkare shi a Kano amma ya kwashe dukiyarsa. Buratai ya samu bayanan sirri na soji don k**a mutumin amma ya boye lamarin lokacin da mutumin ya yi barazanar bankada.

"Sun shawarci Buratai da ya kyale shi ko kuma ya samo hanyar da za a bi don sasanta lamarin. Wadanda abin ya shafa suna Kano da Abuja," wata majiya mai karfi ta shaida wa SaharaReporters.

SaharaReporters a ranar Juma’a ta ruwaito cewa, hukumar ICPC ta tabbatar da kwato kudade, motoci da sauran kayayyaki na biliyoyin Naira daga hannun wani dan kwangilar soja a zamanin burutai.

Azuka Ogugua, kakakin hukumar ne ya bayyana kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

ogagua ya bayyana wanda ake zargin a matsayin Manajan Darakta na K Salam Construction Company Nigeria Limited, Mista Kabiru Sallau.

SaharaReporters ta ruwaito yadda jami’an hukumar ICPC a ranar Alhamis din da ta gabata s**a mamaye wata kadara a Abuja, inda s**a kwato kudade, motoci da agogon hannu na biliyoyin naira daga hannun wani mutum da ya ce na Buratai ne.

Majiya mai tushe ta ce hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta sanar da cewa hukumar leken asiri ta kasa (NFIU) ta yi awon gaba da kudaden a yayin binciken Kabiru.

Daga nan ne NFIU ta mika lamarin ga ICPC, inda ta tura jami’anta domin mamaye gidansa da ke Wuse 2 na babban birnin tarayya Abuja.

SaharaReporters ta tattaro cewa makudan kudaden na daga cikin biliyoyin Naira da aka ware domin siyan mak**ai da alburusai da gwamnatin Muhammadu Buhari ke jagoranta.

Wata majiya ta shaida wa SaharaReporters a ranar Alhamis cewa: “A makon jiya ne jami’an ICPC s**a kai farmaki wani gida da ke Unguwar Wuse a Abuja, kusa da Jami’ar National Open University, inda s**a k**a wani mutum mai suna Kabiru Salisu (Sallau) bayan sun ga tsabar kudi Naira miliyan 850 a gidan,” k**ar yadda wata majiya ta shaida wa SaharaReporters a ranar Alhamis.

“Ya ce kudin na Tukur Buratai ne wanda ke Cotonou a lokacin.

“Jami’an ICPC sun kai shi ofis inda aka kuma gano wasu tsabar kudi Naira biliyan daya. Haka kuma an kwato motoci masu hana harsashi, BMW, G-Wagon da kudinsu ya kai N450m.”

Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Ogugua ya ce bisa ga bayanan sirri, hukumar ta kai samame gidan da ke Wuse 2, Abuja, inda aka gano kayayyakin masu tsada.

Wata majiya a baya ta ce hukumar na fuskantar matsin lamba kan ta rage kudin da aka samu a gidan tsohon hafsan sojin zuwa kasa da Naira miliyan 30.

BACEWAR KUDADEN MAKAMAI

A watan Maris na 2021, mai ba Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno ya bayyana cewa ba a ga wasu kudade da s**a kai biliyoyin naira da aka ware don siyan mak**ai da alburusai a karkashin shugabannin ma'aikatan da s**a shude ba.

tonon sililin nasa ya zo ne ‘yan watanni bayan shugaba Buhari ya maye gurbin Buratai da wasu hafsoshin tsaro.

Sauran sun hada da tsohon babban hafsan tsaro, Gabriel Olonishakin; Shugaban hafsan sojin sama, Abubakar Sadique da babban hafsan sojin ruwa, Ibok Ibas.

A cewar Monguno, kudi ko mak**an ba su kasance a kasa ba a lokacin da aka nada sabbin shugabannin tsaron.

“Yanzu da shi (Shugaba Buhari) ya kawo sabbin mutane (shugabannin ma’aikata), da fatan za su bullo da wasu hanyoyi... Ba wai ina cewa tsofaffin shugabannin ma’aikata sun karkatar da kudaden ba, amma kudin sun bata. Ba mu san ta yaya ba., ”in ji shi.

“Tabbas shugaban kasa zai binciki lamarin. Yayin da muke magana, kungiyar gwamnonin Najeriya su ma suna mamakin inda duk kudaden s**a tafi. Ina mai tabbatar muku da cewa shugaban kasa ya dauki al'amuran tsaro da muhimmanci.

“Gaskiyar lamarin ita ce binciken farko ya nuna cewa kudaden sun bace kuma ba a ga kayan aikin ba.

"Lokacin da sabbin shugabannin ma'aikata s**a k**a aiki, sun kuma ce sun ga wani abu a kasa.

Shin Idan Aka Baka Kudi Naira Na Gugan Naira Har 20,000 Shin Zaka Sayar Da Kuri'arka?
27/06/2022

Shin Idan Aka Baka Kudi Naira Na Gugan Naira Har 20,000 Shin Zaka Sayar Da Kuri'arka?

RAYUWA KENANA garin Ningi jihar Bauchi, akwai wani bawan Allah mai tabin hankali, ana kiransa da sunan Madman, babu wand...
26/06/2022

RAYUWA KENAN

A garin Ningi jihar Bauchi, akwai wani bawan Allah mai tabin hankali, ana kiransa da sunan Madman, babu wanda ya san asalinsa, an ganshi a garin Ningi kusan shekaru 40 da s**a wuce

Wasu na cewa Madman asalinsa dan Kasar Kamaru ne, amma babu tabbaci, mutum ne mai ilmi, yana da zurfin ilmin boko, a duk lokacin da ka ganshi zaka ga takardu a aljihunsa yana ta rubutu, turancinsa ma irin na iyayenmu ne da s**ayi karatu a hannun Turawan mulkin mallaka

Akwai masu cewa wannan mutumi karatu ne ya haukatar dashi, wasu kuma suna cewa asiri aka masa ya haukace ya baro Kasarsu zuwa Nigeria garin Ningi, amma duk wannan dai babu tabbaci, domin babu wanda ya san daga ina ya fito

Cikin ikon an samu wani matashin 'dan siyasa Honourable Audu Bola Ningi ya dauki nauyin kaishi asibitin mahaukata aka masa jinyar tabin hankali ya warke, ba shakka Audu Bola yayi babban jihadi, nayi murna da farin ciki sosai Wallahi, domin na san Madman kusan shekaru 30 da s**a wuce a mai tabin hankali, sai gashi yau Allah Ya bashi lafiya

Abinda Audu Bola Ningi yayi ya k**ata ya zama abin koyi garemu ga duk wanda ya samu dama da iko

Allah Ka saka masa da Aljannah

Kimanin Naira Milyan ukku da dubu dari hudu ne aka raba domin sayen ragunan sallah ga shuwagabannin yakin neman zabe na ...
26/06/2022

Kimanin Naira Milyan ukku da dubu dari hudu ne aka raba domin sayen ragunan sallah ga shuwagabannin yakin neman zabe na Abbas Umar Masanawa na kananan hukumonin talatin da hudu dake fadin Jihar katsina.

✍️ Abdulrashid Musa

Kamar yadda ya bayyana, a ya yin gudanar da taron tare da Shuwagabannin kananan hukumonin talatin da hudu na yakin neman zaben Alh. Abbas Umar Masanawa. Wanda ya nemi tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a zaben fitar da gwani na jam'iyyar Apc.

Babban Daraktan yakin neman zaben Alh. Mamman yaro Batsari yace" Abbas Umar Masanawa yana nan cikin APC Daram dam shida Kwamitin yakin neman zaben sa.

Wanda hakan ne ma yasa shi yake shawarar bayar da wani dan tallafi ga shuwagabannin yakin neman zaben sa na kananan hukumonin talatin da hudu na Jihar katsina. Domin su sayi ragunan sallah, Ya Kuma yi godiya akan yadda s**a ba shi dama a lokacin zaben fitar da gwani da ya gabata.

Shima da yake tofa albarkacin bakin sa tsohon Shugaban karamar hukumar katsina Hon Bala Saulawa wanda yana daga cikin yan kwamitin yaja hankalin sauran ƴan kwamitin dasu zamo masu amana a koda yaushe. Domin samun nasara a rayuwar su.

Da yake jawabin godiya tsohon Shugaban jam'iyyar Apc na karamar hukumar katsina Kuma shugaban shiyyar katsina na yakin Neman zaben Abbas masanawa Hon. Babangida shinkafi ya bayyana godiyarsa a madadin sauran shuwagabannin yakin neman zaben na kananan hukumonin tare da kara nuna goyan bayansu ga dan takarar.

Taron ya samu halartar dukkan daukacin shuwagabannin kananan hukumonin talatin da hudu na yakin neman zaben Alh. Abbas masanawa da sauran yan tafiyar tasa.

An gudanar da taron a yau Asabar 25/06/2022 a Office din yakin neman zabensa dake bisa ring road dake nan cikin birnin Katsina News Now

Tabbas Zan Koma PDP Idan Aka Ki Karbar Kujerata A Ba Ni Kayata A  APC ~ Inji Ahmad Lawan
17/06/2022

Tabbas Zan Koma PDP Idan Aka Ki Karbar Kujerata A Ba Ni Kayata A APC ~ Inji Ahmad Lawan

DA DUMI-DUMI: Akwai Yiwuwar Ministan Sadarwa Da Tattalin Arziki Sheikh Isa Pantami Ya Zama Mataimakin Bola Ahmad TinubuM...
16/06/2022

DA DUMI-DUMI: Akwai Yiwuwar Ministan Sadarwa Da Tattalin Arziki Sheikh Isa Pantami Ya Zama Mataimakin Bola Ahmad Tinubu

Majiyarmu ta tabbatar wa da jaridar Daily News Hausa cewa akwai yiwuwar shugaban kasa Buhari ya zabi Minista Pantami domin ya yiwa Bola Ahmad Tinubu mataimakin shugaban kasa.

Bola Tinubu ya bawa shugaban kasa wuka da nama domin ya zaba mishi wanda zai mishi mataimaki, bincike ya tabbata cewa shugaban kasar ya maida hankali a tsakanin jihohin Bauchi ko Gombe.

Koma dai menene zuwa gobe jam'iyyar za ta bayyana wanda zai yiwa Tinubu mataimaki.

Shin ko kuna fatan hakan ta kasance?

~ Daily News Hausa

16/06/2022

DA ƊUMI-ƊUMI: An Zaɓi Gwamna Ganduje A Matsayin Mataimakin Bola Tinubu

Rahotanni sun ruwaito cewa, jam'iyyar APC sun ɗauki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mataimakin ɗan takarar Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Daily Independent sun ruwaito cewa, masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sun ɗauki Ganduje ne ya zama mataimakin Tinubu a babban zaɓen 2023 saboda halaccin sa ga jam'iyyar da kuma manyan ayyukan da ya yi a jihar Kano.

A wani jawabi da ya sanar da manema labarai, daraktan ƙungiyar magoya bayan Ganduje, Suleiman Magaji ya bayyana cewa, an yi la'akari da batun addini a yayin zaɓen, amma yan Najeriya na buƙatar wanda zai kawo gagarumin cigaba maimakon batun addini.

Daga Mukhtar Lawan Liver Gwarzo

Ƴan Bindiga Sun Shigo Cikin Garin Katsina Sun Sace Mutum TakwasƳan Bindiga Dauke Da Bindigogi Sun Shiga Unguwar Shola Da...
14/06/2022

Ƴan Bindiga Sun Shigo Cikin Garin Katsina Sun Sace Mutum Takwas

Ƴan Bindiga Dauke Da Bindigogi Sun Shiga Unguwar Shola Dake Bayan Asibitin Koyarwa Ta Gwamnatin Tarayya, Katsina Inda S**a Yi Awan Gaba Da Mutum Takwas.

Majiyar Focus News Hausa Ta Shaida Mata Cewa Ƴan Bindigar Sun Shigo Unguwar Shola, Bisa Babura Kusa Da Makabarta Da Misalin Karfe 4: 00 Na Asubuhin Yau Talata, Inda S**a Rinka Bin Gida-gida, Ba Su Kashe Kowa Ba Amma Sun Tafi Da Maza Bakwai Da Mace Daya.

"NA YI MAFARKI ALLAH YA GINAWA TINUMBU KATAFAREN GIDA MAI BENE HAWA DUBU SABA'IN A GIDAN ALJANNAH" - HAJIYA SA'ADATUDAGA...
13/06/2022

"NA YI MAFARKI ALLAH YA GINAWA TINUMBU KATAFAREN GIDA MAI BENE HAWA DUBU SABA'IN A GIDAN ALJANNAH" - HAJIYA SA'ADATU

DAGA Shafin Dokin Ƙarfe TV

Wata ƴar fafutukar yayata manufofin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinumbu, Hajiya Sa'adatu Dogon Bauchi ta labarta cewa a daren jiya ta kwanta barci ta yi mafarkin Allah ya ginawa TINUMBU wani makeken katafaren gida na alfarka a gidan Aljannah wanda tsayinsa ya kai bene hawa dubu saba'in saboda mulkin adalci da aka nuna mata ya yi bayan zamansa shugaban ƙasa na shekaru 8 a Nigeria.

Hajiya Sa'adatu ta bayyana haka ne ya yin wata tattaunawarta da kafar sadarwa ta Dokin Ƙarfe TV, "Haƙiƙa Allah ya nuna min wani katafaren gida a Aljannah an kuma nuna min cewa na Tinumbu ne, haka zalila na kuma ga wasu fararen mutane jajawur cikin fararan kaya sun kewaye Tinumbu a gidan da na yi tambaya su waye waɗannan sai aka ce mun ai su Kashim Shettima da Ganduje ne, da na tambayi dalilin haɗuwarsu sai aka ce ai su ne waziransa a gidan duniya lokacin da ya ke shugaban ƙasa, kuma sun taimaka masa wajen magance matsalolin ƙasar". Cewar ta.

Dogon Bauchi ta cigaba da cewa a lokacin da Tinumbu ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Nageriya ya samu ƙasar matsaloli sun addabe ta, k**ar matsalar tsaro da cin hanci da rashawa da rashin aikin yi, amma ya na hawa ko shekara ba a yi ba ya magance matsalolin ƴan Nageriya su ke rayuwa k**ar a Saudiyya wanda hakan shi ne silar samun wannan gida a Aljannah k**ar yadda ta gani a mafarkin, Inji ta.

Me za ku ce?

Shima fa Kwankwaso Ya kafa Gwamnoni a Yankinsa Kamar yadda Tinubu Yayi kawai dai... Daga Khadija Garba SanusiKamar yadda...
13/06/2022

Shima fa Kwankwaso Ya kafa Gwamnoni a Yankinsa Kamar yadda Tinubu Yayi kawai dai...

Daga Khadija Garba Sanusi

Kamar yadda ake ta Yamaɗaɗi cewar ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Lagos Sanata Bola Tinubu ya kafa Gwamnoni a yankinsa na Yarabawa shiyasa ya samu damar amfani da yaran nasa wajen samun tikitin takarar shugaban ƙasa a Jam'iyya mai mulki to fa shima Ɗan Takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar NNPP kuma Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso haka ya Kakkafa Gwamnoni a nasa yankin na Arewacin Nigeria kawai dai shi kwankwaso ya tsinci kansa ne acikin Al'ummar da basu ɗauki Butulci abakin komai ba kuma Al'ummar da s**a ɗauki sarar nakaika Inuwa ka Kaini Rana, Al'ummar da s**a zamo tamkar Macijin da zaka kiwata daga baya ya sareka.

Barrister Simong Bako; Gwamnan Jihar Plateau na yanzu kuma shugaban Gwamnonin Arewa Barrister Simong Bako Lalong yana ɗaya daga cikin Gwamnonin da kwankwaso ya kafa da hanunsa domin takarar Lalong ta Farko a 2015 ko office na Campaign Bashi da shi ballantana kuɗin sayen Form na Jam'iyyar APC a Chamber ɗinsa ta aikin Lauya yake gudanar da abubuwansa na siyasa, Kwankwaso ne ya saya masa Form na Takarar Gwamna sannan ƙungiyar Kwankwasiyya ta Plateau state ta bashi kyautar office ɗinta na Badamasi Plaza dake Bauchi Road acikin garin Jos domin yayi harkokinsa na siyasa sannan kuma Kwankwason ya tsaya kai da fata domin ganin Barrister Simong Bako Lalong ya tsallake a zaɓen cikin gida na Jam'iyyar APC wanda Badon Kwankwason ba da Solomon Dalung yayi ƙasa-ƙasa da Simong Lalong saboda yafishi kuɗi kuma yafi sanuwa acikin Al'umma amma haka kwankwaso ya shiga ya fita sai da Simong Lalong ya tsallake dukka zaɓubbukan 2015.

Badaru Abubakar; Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar Talamiz duk da kasancewarsa Hamshaƙin mai kuɗi amma saura kaɗan tikitin takarar Gwamnan Jihar Jigawa ya kubce masa a 2015, Allah ya Tarfawa garinsa nono ne bisa ɗaukin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai masa, domin a lokacin har an ayyana Barrister Hassan Hadejia amatsayin wanda zai tsayawa APC takarar Gwamna a jihar Jigawa saboda rikici yaƙi ci yaƙi cinyewa tsakanin Badaru da Ubale to amma shi Barrister Hassan Hadeja da kansa yace bazai iya takarar Gwamna ba saboda bashi da kuɗi gashi kuma Jam'iyya mai mulki ta PDP zai tunkara hakan tasa rikici ya dawo ɗanye nan da nan Kwankwaso yakaiwa Badaru ɗauki kuma Allah ya taimake shi ya samu tikitin takarar Gwamna a jihar Jigawa cikin Jam'iyyar APC kuma Kwankwason bai rintsa ba sai da Badaru ya zama Gwamna a Jigawa wasu na ganin tsoma Hanun kwankwso dumu-dumu a siyasar Jigawa ta 2015 wanda yayi sanadiyyar faduwar Gwamnatin Sule Lamiɗo itace ta ƙara ta'azzara adawar siyasa tsakanin Sule Lamiɗon da Kwankwaso wacce har yanzu take ci Ganga-Ganga.

Nasiru Ahamad el-rufai; k**ar dai a Jihar Jigawa itama Jihar Kaduna abunda ya faru kenan tsakanin Nasiru elrufai da Shehu Sani, rikici ya kaure tsakaninsu kan wanda zaiyiwa APC takara a Jihar Kaduna shima dai Kwankwason ne yaje ya dafawa Nasiru elrufai domin ganin ya riƙewa APCn tutar takarar Gwamna a 2015 a Jihar Kaduna kuma hakan akayi Allah ya bashi Sa'a da taimakon Kwankwaso ya zama ɗan Takarar kuma Kwankwaso bai huta ba saida Nasiru ya zama Gwamna a Jihar Kaduna duk da barazar da s**a sha daga hannun Gwamna Maici Lamaran Yero wanda ya dinga ikirarin idan yaga dama sai ya rushe gidan el-rufai.

Abdullahi Umar Ganduje; a jihar Kano basai nace komai ba game da irin Gudun mowar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayar wajen Tabbatuwar Gwamna Ganduje akan Kujerar Gwamnan Jihar Kano domin zai zamo k**ar ɓata baki ne babu abinda baku sani ba, abunda zan ƙara akai kawai shine a yau duk wani ɗan siyasa da Ludayinsa ke kan dawo a siyasa jihar Kano idan ka cire Sanata Mallam Ibrahim Shekarau to gaba dayansu Rainon Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne rankatakaf babu ragin ɗaka.

To yanzu kuyi tunani da'ace waɗannan Gwamnonin Simong Bako Lalong,Badaru Abubakar,Nasiru elrufai da Ganduje sun tsayawa Kwankwso akan Lamuransa na siyasa da yake buƙatar yanzu a tsaya masa k**ar yadda ya tsaya musu a nasu lamuran na siyasa a lokacin da suke buƙatar a tsaya musu ɗin kwatankwacin yadda Gwamnoni yaran Tinubu s**a tsaya masa a yanzu da yake buƙatar tsayawarsu tunda shima ya tsaya musu a lokacin da yake da damar tsaya musu kuma suke buƙatar a tsaya musu ɗin. MENENE ZAI FARU?

Sannan kuma kuyi Tunanin da ace Gwamnoni da Tinubu ya kafa sun Butulce masa a yanzu da yake buƙatar taimako k**ar yadda Gwamnonin yaran Kwankwaso s**a Butulce masa a daidai lokacin da yake buƙatar taimakonsu, MENENE ZAI FARU?

Rashin kunyar da ake cewa Muna da ita. An san cewa zamuyi dai dai ne, ba zamubi san ra'ayin wasu mutane ba shiyasa.... I...
13/06/2022

Rashin kunyar da ake cewa Muna da ita. An san cewa zamuyi dai dai ne, ba zamubi san ra'ayin wasu mutane ba shiyasa.... Inji Dr. Dikko Umar Radda.

✍️ Abdulrashid Musa

Dr. Dikko Umar Radda Dan takarar gwamnan jihar Katsina a jam'iyyar Apc ya bayyana haka ne, a ranar Lahadi 12/06/2022. A ya yin da yake ganawa gami da liyafar cin abinci da aka shirya ma delegate's mutum dari biyar da shidda wanda s**a zabe shi a zaben fitar da gwani na jam'iyyar Apc. A babban ofishin yakin neman zaben shi dake Jihar katsina.

Dr. Dikko ya kara da cewa" yana da tabbacin yin abinda ya dace ga al'ummar Jihar katsina. Ganin haka ake ganin Baza'a iya juya shi bane shi yasa wasu suke ganin cewa baya da kunya. Ya Kara rokon Allah ya basu iKon sauke nauyi al'umma Jihar katsina idan sun samu nasara.

Daga karshe ya godewa delegate's din da s**a zabe shi tare da basu tabbacin cewa sune zasu shiga gaba domin su zama jakadun shi daga wuraren da s**a fito domin ganin an kai ga nasara a zaben 2023. Ya Kuma gode masu akan damar da s**a ba shi.

Shi ma da yake dofa albarkacin bakinsa mai magana da yawun jam'iyyar Apc na Jihar katsina Alh. Shamsu Sule Dugaji yace"a wannan karon siyasar da zasuyi ta gidan Dr Dikko siyasa ta masu mutunci. Ba zasu yarda a rinka cin mutuncin mutane ba, Kuma baza su lamuci haka ba

Taron yasa masu din bin magoya bayan Dan takarar gwamnan daga ko'ina a jihar Katsina. Tare da Daraktan yakin neman zaben Dan takarar gwamnan Hon. Jabiru Salisu Abdullahi matasa maza da mata da delegate's da dai sauransu.

Duk Ɗan Jam'iyyar APC Da Ya Halarci Taron Da Ake Zagin Shugaba Buhari Da Gwamna Masari Sai Mun Kore Shi Daga Jam'iyyar K...
13/06/2022

Duk Ɗan Jam'iyyar APC Da Ya Halarci Taron Da Ake Zagin Shugaba Buhari Da Gwamna Masari Sai Mun Kore Shi Daga Jam'iyyar Komin Girmansa, Cewar Bala Abu Musawa

Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa (Cigarin Musawa) ya gargadi duk wani mai riƙe da wata kujera ko mai neman wata kujera a ƙarƙashin Jam'iyyar APC a jihar Katsina da ya halarci wani taro ko gangami da ake zagi ko aibata shugaban kasa Muhammadu Buhari da adalin gwamna Alhaji Aminu Bello Masari, Jam'iyyar APC a jihar Katsina za ta kore shi, idan kuma wani mukami ya ke nema za ta tabbatar bai yi wa Jam'iyyar takara ba a zaɓen shekarar 2023.

Alhaji Bala Abu Musawa ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da wasu asibitoci da tituna da matashin dan kwangilar nan, dan asalin karamar hukumar Malumfashi ya gina a mahaifarsa, Alhaji Muntari Sagir da Gwamna Aminu Bello Masari ya jagoranci kaddamar wa yau Asabar a garin Malumfashi ta jihar Katsina.

Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na jihar Katsina, wanda ya wakilci Shugaban Jam'iyyar APC na jihar Katsina a wajen taron ya ce Jam'iyyar APC ta gudanar da zaɓukan fitar da gwani a matakai Daban-daban a wani wuri mun yi dai-dai ba kuma a rasa wurin da muka yi kura-kurai na ajizanci. Abubuwa da ke faruwa bayan kammala zaɓukan, Jam'iyyar APC zaune lafiya take kuma ba mu tunanin faɗuwa Zaɓe saboda mun tsaida nagartattun yan takara a matakai daban-daban.

Alhaji Bala Abu Musawa (Cigarin Musawa) ya kara da cewa Jam'iyyar APC a jihar Katsina ba za ta zura ido ba ga duk wani zababbe ko wani dan majalisa ko shugaban karamar hukuma ba ko mai son tsaya wa takara ba, ya halarci wani taro da ake zagi ko aibata shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello ba, za mu dauki kwakkwarar Mataki kansa na kora komin girmansa.

Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa ya cigaba duk wanda ya faɗi zabe idan har ya yarda da Allah ya taho ayi wannan tafiya da shi, idan kuma ya ji bai iyawa to ya yi zamansa, Saboda ko da shi ko babu shi ina da yakinin Jam'iyyar APC za ta ci zabenta da yardar Allah a shekarar 2023

Salon kwanciyar junediya ya kawo CECE kuce
12/06/2022

Salon kwanciyar junediya ya kawo CECE kuce

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zinariya hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Convenience Store?

Share