03/10/2022
SUN FARA BÓYE GASKÍYA TÚN DAGA YANZÚ
DAGA Dattí Assalafíy
Jíya càbals a gídan síyasar Kaka Bóla Tìnúbú sún fítar da wanì gajéran bidiyó a shafínsa na Faćebook wanda baí wuce second 6 ba s**a nuna Tinubu akan keken mótsa jiki irin na marassa lafiya da ake ajiyewa a Asibití
A cikin bidiyon, sun karyata labarin cewa Tinubu ya rigamu gidan gaskiya a Asibitin da yake jinya a London, sunce bai janyé daga takaran shugaban Kasa ba wai ya warware gashi nan ma yana motsa jiki, kuma ya shiryar zai shugabanci Nìgeria.
Abu na farko, menene abin boyé gaskiya game da rashin lafiyar mutum? kowani bil'adama yana rashin lafiya, kuma kowa zai mutu idan kwanansa ya kare.
Kuma me yasa bidiyón s**a daukeshi second 6 kacal? kamata yayi suyi bidiyo na minti 10 yana motsa jiki, sannan duk wanda ya kure wa bidiyon ido da kyau akayi zooming dinsa za'a ga alamar tambarin asibiti, Likititocin Physiotherapist suna yiwa wadanda suke fama da jinyar Paralysis irin wannan dabi'ah na motsa jiki.
Tìnúbú yayi tsufan da ba zai taba iya rike Nigeria ba, akwai wanda idan tsufa yayi tsufa za'a ga yana karkarwa kamar yadda wannan yake yi, tsufansa da rashin lafiyarsa a bayyane suke, amma karfi da yaji suna son su boye gaskiya saboda su daura mana marar lafiya domin su cigaba da cin amanar da s**a saba.
Abu mafi muhimmanci ga rayuwar Tinubu shine a kaddamar da takaran shugaban Kasa yana nan, amma jam'iyyar APC ta dage saboda dan takaranta yana jinya a Asibiti.
Kwamítín zaman lafiya na 'yan takaran shugaban Kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban Kasa Abdussalam Abubakar ya jagoranci zama da dukkan 'yan takaran shugaban Kasa domin su sanya hannu, kowa yazo ya sanya hannu amma banda Tinubu saboda lalura na rashin lafiya, inda kalau yake babu abinda zai hanashi zuwa ya sanya hannu.
Kacíya da zafi, an shamu mun warké ba za'a kuma ba, yaudaran da aka mana ya isa haka, ba zamu bari ku sake yaudaran mu ba Insha Allah.
Kaka Tinubu اللهم يشفيك