Umar Bakoji

Umar Bakoji Young Physiologist

Re-election For ResittingZannan Hakimin Kasar Galambi
22/01/2024

Re-election For Resitting

Zannan Hakimin Kasar Galambi

Once upon a time as an undergraduate
21/01/2024

Once upon a time as an undergraduate

18/01/2024

Ansoke Kayan LEFE A Kano

18/01/2024
Good Morning This Morning!!!
18/01/2024

Good Morning This Morning!!!

Mutumin nan da ya ki yarda ya sayar da kekensa a Saudiya kan naira miliyan 40, ya bayar da keken a Legas, ga gidan tarih...
17/01/2024

Mutumin nan da ya ki yarda ya sayar da kekensa a Saudiya kan naira miliyan 40, ya bayar da keken a Legas, ga gidan tarihi na kasa da ke cikin garin Legas.

Yanzu haka dai Alhaji Ali Obobo ya fara tattaki daga birnin Legas inda zai tafi birnin Maidugurin jihar Barno a kasa.

Keken da ya hau yaje Makkah daga Jos, yayi Umara, wani balaraben kasar Egypt ya saya naira miliyan 40 amma ya ki siyasarwa, yanzu haka keken na gidan tarihi a Legas, ya ce yayi haka ne saboda kishin kasa.

Wani fata kuke masa?

17/01/2024

Dokar Da Tahana Yin Kayan Kefe AKano.... Da hukuncin kowata Laifi bayan an Aikaya

Good Morning This morning
17/01/2024

Good Morning This morning

ALHAMDULILLAH
12/01/2024

ALHAMDULILLAH

Muna Godiya Da Ziyarar Bazata Mai Girma
12/12/2023

Muna Godiya Da Ziyarar Bazata Mai Girma

Ba Na Nadamar Kashe Mahaifiyata Ba –MatashiWani fusataccen matashi da aka bayyana sunansa da Sadiq Idrissu, ya kashe mah...
12/12/2023

Ba Na Nadamar Kashe Mahaifiyata Ba –Matashi

Wani fusataccen matashi da aka bayyana sunansa da Sadiq Idrissu, ya kashe mahaifiyarsa a Jihar Adamawa, da ya bayyana cewa bai yi nadamar kisan gillar da ya yi mata ba.

Matashin dan shekaru 30, ya kashe mahaifiyarsa ne ranar 05/12/2023, a garin Boga cikin karamar hukumar Gombi a jihar, maimakon nadama kan kisan gillar da ya mata, amma cewa “ban yi nadamar kisan da na yi wa mahaifiyata ba” in ji matashin.

Ya ci gaba da cewa “na kashe ta ne, saboda ta bayyana min ita mayya ce, da ma jama’a na zarginta da maita, kuma gaskiya ne, domin tana aikata wasu abubuwan mamaki, musamman da daddare.

“Mamana tana bayyana min a cikin mafarki a matsayin mayya, tana kuma jefa min tsoron da ke hana ni yin bacci da daddare” in ji matashin.

Ya ce ranar da abin ya faru “na dawo gidanmu cikin dare, sai ban same ta a dakinta ba, sai ‘yar uwata ke kwance, na shiga dakin babana ban same ta ba, saboda haka na fita neman ta a waje na same ta kuma nan take na harbe ta sau biyu, tunda na tabbata ita mayya ce” in ji shi.

Leadership ta ruwaito cewa Ita ma rundunar ‘yansandan jihar ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ta tabbatar da lamarin, ya ce matashin ya kashe mahaifiyarsa bisa zargin ita mayya ce

Ya ce bayan kammala bincike rundunar za ta gurfanar da matashin gaban kuliya

DA ƊUMI - ƊUMI: Rarara ya yi kira ga Al'ummar Jihar Kano da su yi murnar Nasarar Gawuna cikin natsuwaFitaccen mawakin Si...
12/12/2023

DA ƊUMI - ƊUMI: Rarara ya yi kira ga Al'ummar Jihar Kano da su yi murnar Nasarar Gawuna cikin natsuwa

Fitaccen mawakin Siyasa a nahiyar Afrika, Dauda Kahutu Rarara ya yi kira ga Al'ummar Jihar Kano, da za su fito murna a lokacin da za a bayyana nasarar karshe ta Gawuna/Garo da su fito cikin natsuwa ba tare da tada hankalin kowa ba.

A cewarsa, babu abin da su ke so irin ci gaban Jihar Kano, don haka za su fito murna bayan yanke hukuncin karshe, amma ba za su fito don tada hankalin kowa ba, ko kuma don kona dukiyar kowa ba, ko yin wata hayaniya da za ta sanya Al'umma dar-dar ba.

Rarara ya bayyana haka ne a wani gaggarumin taro da ya shirya a jiya Litinin, 11 ga watan Disamba 2023 dakin taro na Otal din Bristol da ke Kano.

Sannan ya yi wa masoyansa albishir da sabuwar wakar sa da zai saki mai taken 4-0.

Sako Daga Abdullahi Al-Hikima

12/12/2023
10/12/2023
Assalamualaikum! Fatan Kowa Nacikin Koshin Lfy Amin Kamar Yadda Kukasani Cewa *Court of Appeal Hadida Hukumar Zabe (INEC...
04/12/2023

Assalamualaikum! Fatan Kowa Nacikin Koshin Lfy Amin Kamar Yadda Kukasani Cewa *Court of Appeal Hadida Hukumar Zabe (INEC)* Ta Tabbatar da Sake Zabe Awasu Mazabu Na Yankin Zungur Galambi da MIRI Ciki Harda Rugan Kela "Wacce tana Daya Daga Cikin Manyan Mazabu A Galambi Ward Kuma Yankin *Halartaccen Dan Majalisa* "Alh. Saidu Yusuf".......... Da Wannan Nake Kira Ga Alumman Wannan Kungiya (Galambi Students Association) da Mutaya Uban Gidanmu da Addua, Campaign dadai Sauran Ababuwan Das**a Dace. Allah Yamana Jagora Amin

Yadda Abba Gida-Gida Ƙawata Shataletalan Dake kofar Gidan GwamnatinWane fata zakú yi masa?
27/11/2023

Yadda Abba Gida-Gida Ƙawata Shataletalan Dake kofar Gidan Gwamnatin

Wane fata zakú yi masa?

Na Rantse Da Allâh Mahaifiyata Ce Tace Min Idan Naje Wajén Muƙabala Bata Yafe Min Ba, Hakań Yasa Nayi Mata Biyayya Naƙi ...
27/11/2023

Na Rantse Da Allâh Mahaifiyata Ce Tace Min Idan Naje Wajén Muƙabala Bata Yafe Min Ba, Hakań Yasa Nayi Mata Biyayya Naƙi Zuwa Wajen, Cewar~Idris Dutsen Tanshi

Me zaku ce ?

26/11/2023

YANZU - YANZU: Har yanzu dai babu Dr. Idris Abdulaziz, babu shi babu alamar sa ko wakilcin a wurin taron Muƙabalar da take gudana yanzu haka a birnin Bauchi, wanda hakan ya sanya mutane suna ta cewa Dr. Idris Abdulaziz kodai yaji tsoro ko kuma dama cika baki kawai yake yi.

Shin menene ra'ayinku kan wannan batu?

Naíra ɗari bìyar 500 ta Halal ba sa'ar Naìra Mìlìyan ɗarí bìyar (500,000,000 ta Haram ba cé, Céwar Sheikh Ahmad Tijjani ...
30/10/2023

Naíra ɗari bìyar 500 ta Halal ba sa'ar Naìra Mìlìyan ɗarí bìyar (500,000,000 ta Haram ba cé, Céwar Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum.

YANZU - YANZU: Ɗan wasa Lionel Messi ya sake lashe kyautar Ballon d'Or na shekarar 2023.
30/10/2023

YANZU - YANZU: Ɗan wasa Lionel Messi ya sake lashe kyautar Ballon d'Or na shekarar 2023.

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Zakir Naik tare da ɗansa sun isa Sokoto bayan  Sarkin Musulmi ya gayyace su don yin ...
30/10/2023

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Zakir Naik tare da ɗansa sun isa Sokoto bayan Sarkin Musulmi ya gayyace su don yin wa'azi a wasu jihohin Najeriya.
📸 - Gwamnatin Sokoto/Aliyu Tilde

Ranar juma'a da yamma ne aka katse layukan sadarwa a Gaza, yayin da Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a yankin.Har yan...
28/10/2023

Ranar juma'a da yamma ne aka katse layukan sadarwa a Gaza, yayin da Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a yankin.

Har yanzu ba a san adadin mutanen da hare-haren s**a kashe ko jikkata ba saboda babu sadarwa da asibitoci.

Mutane na ƙoƙarin tuntuɓar 'yan uwansu a sauran yankuna don jin lafiyarsu, amma ba su iya samun su.

Atiku Abubakar ya fito bainar jama'a karon farko bayan rashin nasara a Kotun ƙoli.Kotun Allah ya isa ta tabbatar da nasa...
28/10/2023

Atiku Abubakar ya fito bainar jama'a karon farko bayan rashin nasara a Kotun ƙoli.

Kotun Allah ya isa ta tabbatar da nasarar Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu.

Tun bayan wannan hukuncin ba a ƙara ganin Atiku ba sai jiya Jumu'a a Abuja.

WATA SABUWA:'SHAWARÁ: Ya Kamata Maza Su Daina Roƙon Ƴan Mata Kuɗi Social MediaWasu sun mayar da roƙon kuɗi a social medi...
27/10/2023

WATA SABUWA:'
SHAWARÁ: Ya Kamata Maza Su Daina Roƙon Ƴan Mata Kuɗi Social Media

Wasu sun mayar da roƙon kuɗi a social media wata sabuwar hanyar neman kuɗi, Cèwar matashiya ƴar gwagwrmaya Zainab Nasir Ahmad

Me zakù cè ?

Get Ready New Otondi
27/10/2023

Get Ready New Otondi

Wai menene abin mamaki don maroƙi ya juya wa wanda ludayinsa ya bar kan dawo baya? Ra'ayin Barista Bulama Bukarti Su fa ...
27/10/2023

Wai menene abin mamaki don maroƙi ya juya wa wanda ludayinsa ya bar kan dawo baya?

Ra'ayin Barista Bulama Bukarti

Su fa dama ba don al-umma ko ma ƙaunar ƴan siyasa suke yi ba. A'a, don aljihunsa kaɗai suke yi. Iya kuɗinka, iya sha'aninka. Da zarar zamaninka ya shuɗe, sai su tattare nasu ya nasu, su arce gurin na gaba. Dama can ya san cewa duk matsalolin da muka yi ta faɗa a kan Buhari gaskiya ne amma ya ƙi Allah saboda yana samu.

Duk kyawawa abubuwan da ya faɗa a kan Tinubu yanzu, ya faɗe su a baya a kan Buhari, kuma haka zai yiwa Tinubun ma idan ya dena samu. Kare ma ya fi maroƙi amana.

Address

Brigade
Kano

Telephone

+2347011903492

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Umar Bakoji posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Umar Bakoji:

Videos

Share

Category


Other Kano convenience stores

Show All

You may also like