14/02/2021
FALALAR AL'UMMAR ANNABI (ﷺ)
***********************************
Hadithi daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace Manzon Allah (saww) yace :
"Hakika Annabi musa (as) lokacin da aka saukar masa da At-Taura bayan ya karantata sai yaga ambaton wannan al'ummar aciki. Don haka sai yace :
"Ya Ubangiji hakika acikin allunan Attaura ni naga ambaton wasu al'ummah wadanda sune na karshe amma kuma sune na farkon wadanda ake karbar cetonsu. (ina so) ka sanya su zama al'ummata".
Sai Allah yace masa "WANNAN AL'UMMAR AHMADU CE (SAWW)".
Sai Annabi Musa (as) ya sake cewa "Ya Ubangijina, hakika ni acikin allunan Attaura naga ambaton wata al'ummah wadanda suke masu amsawa (Wato masu amsa kiran Allah) kuma ana amsa musu (idan sunyi roko). Ina so ka sanya su zama al'ummata".
Sai Allah yace "WANNAN AL'UMMAR AHMADU CE".
Sai ya sake cewa "Ya Ubangijina, Hakika ni acikin allunan Attaura naga ambaton wata al'ummah wadanda littafinsu yana cikin Qirjinsu, Amma suna karantashi azahiri. Ina so ka sanya su zama al'ummata".
Sai Allah yace masa "WANNAN AL'UMMAR AHMADU CE (SAWW)".
Annabi Musa (as) yace: "Ya Ubangijina, hakika acikin allunan Attaura naga wata al'ummah wadanda suna cin ganimar Yaqi. Ina so ka sanya su zama al'ummata".
Sai Allah yace masa "WANNAN AL'UMMAR TA AHMADU CE (SAWW)".
Sai Annabi Musa (as) ya sake cewa : "Ya Ubangijina hakika acikin Allunan Attaura naga wata al'ummah wadanda suke sanya Sadaqoqinsu acikin cikinsu amma kuma ana basu lada akanta. Ina so ka sanya ta zama al'ummata".
Allah yace masa "WANNAN AL'UMMAR AHMADU CE (SAWW)".
Sai Annabi Musa yace "Ya Ubangijina hakika acikin Allunan Attaura naga wata al'ummah wadanda idan 'dayansu ya himmantu akan zai aikata alkhairi amma bai aikata ba, za'a rubuta masa lada guda. Idan kuma ya aikata ta sai a rubuta masa lada goma. Ina so ka sanya ta zama al'ummata".
Sai Allah yace masa "WANNAN AL'UMMAR AHMADU CE (SAWW)".
Annabi Musa (as) ya sake cewa "Ya Ubangijina hakika naga wata al'ummah acikin Allunan Attaura wacce idan dayan cikinsu yayi nufin zai aikata mummunan abu amma bai aikata ba, to ba'a rubuta masa zunubi. Idan kuma har ya aikata to zunubi kwaya daya tal ake rubuta masa. Ina so ka sanya ta zama al'ummata".
Sai Allah yace masa "WANNAN AL'UMMAR AHMADU CE (SAWW)".
Sai Annabi Musa (as) yace "Ya Ubangijina hakika ni naga wata al'ummah acikin Allunan Attaura wadanda za'a basu ilimin farko da ilimin Qarshe kuma su zasu kashe Qahon 'bata wato Masihud Dajjal (Dujal) ina so ka sanya ta zama al'ummata". Sai Allah yace masa "WANNAN AL'UMMAR AHMADU CE (SAWW)".
Daga nan sai Annabi Musa (as) yace "To Ya Ubangiji ka sanyani cikin al'ummar Ahmadu (saww)". To nan take sai aka bashi wasu abubuwa guda biyu. Allah yace masa : "YA KAI MUSA! HAKIKA NI NA FIFITAKA BISA MUTANE DA MANZANCINA DA KUMA ZANCENA. TO KA RIKE ABINDA NA BAKA DA QARFI KUMA KA ZAMA CIKIN MASU GODIYA". (Suratul a'araf ayah ta 144).
Sai Annabi Musa yace "Na yarda Ya Ubangiji".
Abu Nu'aym ne ya ruwaitoshi daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra).
Ya Allah muna godiya agareka da ka sanyamu cikin al'ummar Annabi Muhammadu Ahmadun Hamidun Mahmudun (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ba tare da ko sisinmu ba, sai dai falalarka wacce ka kebancemu da ita.
Daga Zauren Fiqhu 07064213990 08157968686 (14/02/2021).